Almundahana : karya ce babu alkawarin aure tsakanin mu – cewar Hadiza Gabon
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Hadiza Gabon ta musanta alkawarin auren wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa, tare da cin kudin sa har naira dubu dari 396. Jaridar Rfi Hausa na ruwaito
Hadiza Gabon ta musanta batun auren Bala Musa ne bayan da ta gurfana gaban babbar kotun shari’a dake Magajin Gari a jihar Kaduna, inda ta ce bata taba yi masa alkawarin aure ba, hasali ma bata san shi ba kuma bata da wata alaka da shi ta kusa ko ta nesa.
Tun da fari dai mutumin mai suna Bala Musa ne ya gurfanar da Hadiza Gabon a gaban Kotun, inda ya bukaci a kwato masa hakkin sa, bayan da ya ce ta ki auren sa duk da alkawarin da suka yi, bayan kuma ta cinye kudin sa har naira dubu 396.
Hadiza Gabon ta bakin lauyan ta Mubarak Sani Jibril ta ce tsakanin ta da mutumin bai wuce magoyin bayan ta da suka hadu a shafin ta na Facebook ba, amma babu batun soyayya ko alkawarin aure a tsakanin su.
Ya zuwa yanzu dai mai shari’a Khadi Malam Rilwanu Kyaudai ya dage sauraron karar zuwa tanar 28 ga watan yunin da muke ciki, yayin da ya bada belin Hadiza Gabon, bisa sharadin gabatar da mutane biyu mazauna jihar Kaduna.