Uncategorized

Ali Jita Zai Tallafawa Sanin Plumber Mai Kafiyya Domin Ya Zama Fitaccen Mawaƙi

Fitaccen mawaki Ali Jita ya dauki nauyin wakar sabon mawaki Sanin Plumber Mai Kafiyya domin zama fitaccen Mawaki.Salisu Magaji Fandalla’fih

A kwanakin baya ne dai aka yada wakar fasihin mawakin ta shafin TikTok inda Videon wakar ya shahara kuma yaja hankali duba da yadda wakar tai bayani kan abinda ke faruwa a Nigeria.

Sanin Plumber dai yayi wakar ne kan halin da Talakawan Nigeria ke ciki, kamar yadda wani abokin sa ya bayyana suna zaune ne kurum mawakin ya fara yinta kamar da wasa.

A cewar sa sabon mawakin yana iya raira wakoki masu yawa a lokaci guda ba tare da ya rubuta ba kuma tare da kafiyyar su.

Sakamakon yada Videon da yaja hankali fitaccen Mawaki Ali Jita ya nemi sanin inda Sanin yake tare da cewa a kawo shi Studio don ya raira wakar.

A jiya ne dai aka kai mawakin harya fara raira wakar a Studio na Ali Jita wanda ake da yakinin wakar zatai shura duba da yadda wakar tai ma’ana.

Kamar yadda Ali Jita ya bayyana a shafin sa na TikTok yace a yau ne na karbi bakuncin Sanin Plumber a Office ɗina, inda a take aka yi masa kida tare da fara yinta nan take

Wane fata zaku yi masa?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button