Labarai

2023: Ni ba wanda na zaɓa ya zama ɗan takara, a bar dalaget su yi zaɓe – Buhari

Advertisment

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Litinin ya bayyana cewa bai zaɓi kowa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ba.Daily Nigerian hausa ta ruwaito

A jiyah ne dai shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar da shugaban kasa ya fi so ya tsayar a jam’iyyar.

Sai dai a lokacin da yake jawabi ga gwamnonin Arewa 14 a karkashin jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa, Buhari ya ce a bar dalaget su zab5i duk wani ɗan takarar da suke so a babban taron jam’iyyar APC na kasa da ke gudana.

A cewarsa, “ba za a ƙaƙaba wani ɗan takara a jam’iyyar ba.”

Shugaba Buhari ya ce jam’iyyar na da muhimmanci kuma dole ne a mutunta mambobinta yadda su ma za su ji cewa su na da muhimmanci.

Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai Garba Shehu ya fitar ta ce: “Shugaban ya ce ya san me yake yi, ya kuma bukaci gwamnonin APC su san me su ke yi;

“An zabe ku kamar yadda aka zabe ni. Kun san me ku ke yi kamar yadda ni ma na san me na ke da shi. Allah ya bamu dama; ba mu da dalilin yin korafi. Dole ne mu kasance mun samu ɓacin rai kamar yadda mu ke samun farin ciki. A bar dalaget su zabi wanda yai musu. Dole ne jam’iyyar ta sa hannu, babu wanda zai nada kowa,” in ji Buhari.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button