Labarai

YANZU-YANZU: Ƴan Majalisar Dokoki ta Kano 3 sun sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP

Wasu Ƴan Majalisar Dokoki ta Jihar Kano guda uku sun sauya sheƙa da ga jam’iya mai mulki ta APC zuwa jam’iyyar NNPP.

Hakan na kunshe ne a cikin wasikar sauya sheƙar da su ka aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Hamisu Chidari, inda suka sanar da majalisar sauya shekar su daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.

A cikin sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Uba Abdullahi ya rabawa manema labarai, ya ce wasikun masu ɗauke da kwanan watan 5/5/2022, sun isa majalisar, inda ta karɓe su a hukumance.daily nigerin hausa na ruwaito.

Majalisar ta kuma yi musu fatan alheri a bisa mataki na gaba da su ka ɗauka a siyasar su.

A cewar sanarwar, ƴan majalisar da suka koma jam’iyyar NNPP su ne;

1. Abdullahi Iliyasu Yaryasa, mai wakiltar mazabar Tudun Wada.

2. Muhammadd Bello But-Butu,
mai wakiltar mazabar Tofa/Rimin Gado.

3. Kabiru Yusuf Ismail, mai wakiltar mazabar Madobi

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button