Labarai

‘Yan Arewa sun saya wa Jonathan tikitin takarar shugaban kasa

 

TSOHON Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya karbi takardar neman tsayawa zaben shugaban kasar shekara mai zuwa a karkahsin Jam’iyyar APC bayan an dade ana rade radin cewar zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar.rfihausa na ruwaito

Wata hadaddiyar kungiyar Yan arewacin Najeriya ta biya naira miliyan 100 wajen karbar fam din da sunan tsohon shugaban kasar wanda har ya zuwa wannan lokaci bai bayyana aniyar sa ta tsayawa zaben ba.

A kwanakin da suka gabata wasu matasa sun yi zanga zangar lumana a birnin Abuja, inda suka yi tattaki zuwa ofishin Jonathan inda suka bukaci ya bayyana aniyar sa ta tsayawa zaben.

Idan tsohon shugaban ya amince da wannan tayi na tsayawa a karkashin Jam’iyyar APC, takarar sa na iya raba kan ‘yayan Jam’iyyar ganin cewar tuni mutane sama da 25 suka sayi tikitin tsayawa zaben cikin su harda Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da ministan mai Timipriye Sylva.

Gwamnan Bauchi kuma tsohon ministan Birnin Abuja a karkashin Jonathan da yanzu haka yake takarar neman tikitin PDP domin tsayawa zaben shugaban kasar, yace muddin Jonathan ya bayyana aniyar sa ta tsayawa, zai yi watsi da na shi takarar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button