Labarai

Ya Tura Matarsa Karuwanci Akan Kudi Naira Miliyan 1.4M Ya Kuma Sayar Da Dansa Mai Shekaru Biyu Dubu 600,000 Na Naira

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sunyi caraf sun cafke wani matashin magidanci mai shekaru 36 Mai Suna Kingsley Essien bayan da matarsa daya tura karuwanci a kasar Mali ya shigar da karansa.

Matar tashi ta labartawa jami’an tsaro cewa, a shekaran data gabata ne mijinta yace mata ya sama mata aiki mai tsoka a birnin Bamako na Kasar Mali. Tace, “Banyi tunanin komai ba kawai na amince masa na tafi Bamako. Ina zuwa ne wata Mata data kware wajen safaran mutane na ajiye ni a gidanta ta nufi na dinga yin karuwanci bayan data shedamini da sayeni a wajen mijina akan naira miliyan daya da dubu dari hudu”.

Bayan data samu tsarewa ne zuwa ofishin jakadanci na Nijeriya dake Bamako, da taimakonsu ta samu ta dawo gida Nijeriya. Tana dawone ta sanarwa ‘yan sanda inda su kuma suka yi ram da mijin nata.

Ya Tura Matarsa Karuwanci Akan Kudi Naira Miliyan 1.4M Ya Kuma Sayar Da Dansa Mai Shekaru Biyu Dubu 600,000 Na Naira
Ya Tura Matarsa Karuwanci Akan Kudi Naira Miliyan 1.4M Ya Kuma Sayar Da Dansa Mai Shekaru Biyu Dubu 600,000 Na Naira

Sai dai bayan kamashi ne ta nemi jin inda dansu mai shekaru biyu yake wanda ta barshi a karkashin kulawar mahaifinsa. Amma ya sanarwa ‘yan sanda tuni ya cefanar da Dan nasa akan kudi naira dubu dari shidda.

Nan take ‘yan sanda suka tura wanda ake tuhuma shashin binciken masu safaran mutane. Suka kuma bazama neman wanda ya sayi dan domin ceto sa.

Wannan dai labari ne da ya kamata mata su rika sanin irin mazan da zasu aura bayan sun tabbatar da irin sana’ar da suke yi ko aiki domin gudun fadawa irin wannan masifan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button