Labarai

Wani dan Najeriya ya yi yunkurin kashe kansa saboda hasarar Naira miliyan 58 da ya yi a dalilin wata Budurwa da suka hadu a duniyar Facebook

Advertisment

Wani marubuci dan Najeriya, Mista Odibe Emeka wanda ke zaune a unguwar Obosi karamar hukumar Idemili a jihar Anambra, ya shiga halin jimami inda yanzu haka yake ya farfadowa daga yunkurin kashe kansa da yayi. Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Mista Osita ya hadu da budurwa sa ne a Facebook inda ta damfare shi kudi kimanin dala 140,000 kiyasin kudin Najeriya N58million.

Budurwar takasance yar kasar kanada

Budurwar ta kasance mazauniyar kasar Kanada, ta yi masa alkawarin taimaka masa ya buga tare da siyar masa da littafin sa mai suna The Truth, My Journey’.LH na wallafa a shafinta

Kwafi 100,000 da za a fara bugawa za a sayar da su a cikin watanni shida wanda za a samu kudi akalla dala 140,000, da za a yi amfani da su wajen fara gudanar da kamfani na kamar yadda aka tsara a cikin takardar yarjejeniya” “gaba duk wata hanyar da zan sameta ta toshe. ,” in ji shi.

Advertisment

Emeka ya yi yunkurin kashe kansa

Emeka ya sha guba don ya kashe kansa amma aka yi sa’a, iyayensa suka yi gaggawar garzayawa da shi asibitin St. Charles’ Borromeo, Onitsha. Da yake bayyana halin da ya tsinci kansa a lokacin da yake farfadowa ya ce:

Na yi matukar takaici har na yi yunkurin kashe kaina ta hanyar shan guba amma cikin ikon Allah na rayu. Amma har yanzu bata dawo min da kudi na ba.
“Ina neman jama’a da su taimaka min in samu in kwato kudade na dala 140,000 daga hannunta. Kawai za a cuceni saboda an ga ni talakan Najeriya ne.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button