Labarai

Tiktok Ya Fito da Sabuwar Hanyar da Masu Amfani dashi Za su samu kuɗi

 

Kamar de yadda kuka sani Tiktok yana daya daga cikin Social Media Platform wanda yake bada damar masu amfani dashi su wallafa video ta yadda mabiyansu zasu kalli videon da suka dora.

A yanzu Tiktok yana kan gaba wajen amfani dashi musamman wajen samari da yan-mata sai de duk da hakan basu bada damar ana samun kudi dashi ba.

A yanzu de haka Kamfanin na Tiktok ya kaddamar da Tiktok Pulse domin bawa masu amfani dashi damar Samun kudi ta hanyar dora talla akan bidiyon da suke dorawa.

Sai de kuma kafin samun kudi da tiktok dole sai ka cika wasu sharruda kafin su amince dakai ka fara samun kudin. Sharrudan sune kamar haka: Dole sai kana da mabiya wato follower 100’000 sannan zaka sami damar shiga tsarin Tiktok pulse domin ka fara samun kudin.

A yanzu haka wannan tsarin na samun kudi a tiktok za a fara gabatar dashi a America a watan Yuni 2022, Sannan kuma Za a fadadashi acikin watanni masu zuwa

Wannan de shine bayanin da kamfanin tiktok suka fitar ga me da samun kudi ta hanyar amfani da tiktok.

Allah ya baiwa mai rabo Sa’a

Sources: Hikima

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button