Labarai

Saurayina ya ce in ban ba shi kai na ba, zai koma bin karuwai da shaye-shaye – Budurwa

Wata budurwa ta nemi shawarar jama’a akan wani sharadi da saurayinta ya ba ta. A cewarta, har gida ya zo ya sanar da ita tsarinsa, Daily Trust Hausa ta ruwaito.

Ta ce ya bukaci ya ba ta kanta idan ba haka ba zai fita waje ya dinga neman karuwai ko kuma shaye-shaye wanda da ma abokansa sun dade a cikin harkar.

A yadda ta nuna, ba ta son ba shi kanta sannan ba ta son rabuwa da shi, hakan ya sa ta bazama neman mafita.

Ta ci gaba da cewa:

“Saurayina ne ya ke zuwa min da wasu tsare-tsare duk lokacin da ya zo gidanmu.

“Ya ce ko dai in amince da bukatarsa ko kuma idan har na ki yarda zan koma bin karuwai da kuma shaye-shaye saboda dama abokansa sun dade a harkar, shi ne kadai Allah ya tsare.

“Ya ce in har na ki yarda da bukatarsa, karuwai zai koma bi. Don Allah ‘yan uwan na san dai ba zan amince ba amma ya ku ke gani ya kamata in yi?”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button