Kannywood

Na yi nadamar shiga fadan Ali Nuhu da Adam Zango – General BMB

Jarumin fina-finan Hausa, furodusa kuma darekta, Bello Muhammad Bello, BMB, ya bayyana shirinsa na komawa sana’ar fim da kuma tambayoyi dangane da rayuwarsa, LH ta ruwaito.

A tattaunawar da aka yi da BMB, ya gabatar da kansa da farko.

A cewarsa sunansa Bello Muhammad Bello, amma an fi saninsa da General BMB. Furodusa ne shi, darekta ne, sannan kuma jarumi a masana’antar Kannywood.

Ya bayyana cewa ya na rubuta labarin fina-finai. Ya ce ya tashi ne tsundum a rayuwar musulunci a cikin garin Jos da ke Jihar Filato.

Ya ci gaba da cewa:

“Na yi makarantar firamare ta addinin musulunci inda na zarce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Riyom.”

Ya ce ya zarce kasar Jamus inda ya yi karatun boko, daga nan ya wuce Belguim inda ya so zauna gaba daya.

Ya bayyana cewa bayan dawowarsa harkar fim ne ya ga dacewar ya karo ilimi, sai ya koma jami’ar Jos inda ya yi karatun diploma a harkar jaridanci. Daga bisani ya kara komawa ya yi wata diploma a fannin kasuwanci.

A cewarsa a 2005 ya koma fannin tattali inda ya yi degree daga jami’ar Jos.

Yayin da aka tambaye shi dalilinsa na barin harkar fim, cewa ya yi bai bari ba. Yanzu haka ya na ta kokari ne akan sakin fina-finansa masu dogon zango wadanda za su fito nan ba da jimawa ba.

An tambaye shu abinda ya fi faranta masa rai a lokacin yana cikin a harkar fim, anan ne ya kada baki ya ce gayyatarsu da aka yi zuwa kasar Amurka don su karo ilimi.

Bayan an tambayeshi idan akwai abubuwan da ya yi wadanda daga baya a yi nadama a matsayinsa na jarumi, sai ya ce ya ce akwai.

“Maganar gaskiya akwai. Na yi danasanin shiga fadan Jarumi Ali Nuhu da Adam Zango. Na yi kuskure da na saurari bangare daya kuma na yi aiki da abinda na ji ba tare da na saurari dayan ba.

Bayan na gane kuskurena na nemi yafiyar Ali Nuhu, shi da na yi wa laifi. Kuma yanzu haka mu na da alaka mai kyau tsakaninmu. Bayan nan mun ci gaba da abotarmu.”

An tambaye shi batun aure inda ya ce ya yi aure. Akwai wata jaruma wacce ta hasake fim dinsa na ‘Uwar Miji’, ita ya aura.

Ya bayyana yadda Ubangiji ya albarkace su da samun haihuwar tagwaye, yanzu shekarunsu 5 da aure.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button