Labarai

MACE MAI KAMAR MAZA: Binani ta doke tsohon gwamna, tsohon shugaban EFCC a zaɓen fidda-gwani na APC a Adamawa

Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, Aishatu Dahiru, wacce a ka fi sani da Binani, ta lashe zaɓen fidda gwani na gwamnan Adamawa a jam’iyyar APC.

Dahiru ta doke tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, ts karbi tikitin zaɓe a jam’iyyar.

Da yake bayyana sakamako, shugaban kwamitin zaɓen, Gambo Lawan, ya ce Aishatu Dahiru ta samu kuri’u 430 inda ta doke abokin hamayyarta Nuhu Ribadu wanda ya samu kuri’u 288.

Ya ce Bindow ya zo na uku da kuri’u 103, yayin da dan majalisa Abdulrazak Namdas ya zo na hudu da kuri’u 94.

Zaɓen, wanda aka gudanar a gidan sinimar Lamido da ke babban birnin jihar, an fara shi ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Alhamis, inda aka kammala da misalin karfe 8:45 na safiyar yau Juma’a.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, kawo yanzu, Binani ita ce ƴar takara gwamna mace tilo da ta samu tikitin shiga babban zaɓe na 2023.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button