Labarai

Lauyar da tayi bayani kan dokar “Defense of Provocation” don kare masoya Manzo Allah S.A.W a Sokoto ta samu Lambar yabo

An samu mace lauya ta farko daga yankin Arewa Hausa – Fulani da ta samu shiga cikin jerin fitattun matasa 100 da ake karramawa duk shekara a masarautar Ooni da sukayi fice a fannin kyautata jin dadin rayuwar jama’a a fannoni daban-daban na rayuwa kama daga fasaha, kimiyya da kirkire-kirkire, sana’o’i da sauransu. Shafin muryoyi ya ruwaito

Wannan hazikar mace kuwa itace matashiyar lauyar nan da tayi suna a fagen jin kai, wacce aka dade ana damawa da ita a fannin kare yancin mata da yara, Barrister Aysha Ahmad.

Babban Basaraken Kudu “Ooni of Ife”, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya karrama Barrisater Aysha Ahmad da lambar yabo a bikin Royal African Young Leadership Forum (RAYLF) Award.,

Lauyar da tayi bayani kan dokar "Defense of Provocation" don kare masoya Manzo Allah S.A.W  a Sokoto ta samu Lambar yabo
Lauyar da tayi bayani kan dokar “Defense of Provocation” don kare masoya Manzo Allah S.A.W a Sokoto ta samu Lambar yabo

Ayasha wacce a yanzu haka take rike da Daraktan sashen shara’a na hukumar tara kudaden haraji na Kaduna (KADIRS), ta shahara wajen taimakon jama’a da kare hakkin ‘ya’ya mata.

Ta sha samun lambobin yabo da karramawa a lokuta daban-daban a fagen aikinta.

Ko a yan kwanakin nan Barrister Aysha ta samu yabo da addu’oin Alkhairi sosai biyo bayan yadda ta tsaya tsayin daka wajen kare martabar Manzon Allah S.A.W ba tare da shakka ko shayin kowa ba a lokacinda ake tsaka da cece-kuce kan abunda ya faru a Sokoto.

Ooni yace An zabo Aysha ne sakamakon ficen da tayi wajen taimakon al’umma, kwarewar ta wajen aiki, da salon iya jagoranci, da tausayin ya’ya mata da bi masu hakkinsu, kana uwa uba da jajircewar ta da kuma rashin tsoro.

Barrister Aysha ta karbi kambun karramawar ne a dakin taro na Oduduwa Hall dake Obafemi Awolowo University, a ile-Ife.

Rashin tsoro da sanin makamar aiki yasa Barrista Aysha ta fita tayi bayani akan “Defense of Provocation” wanda ya dauki hankalin duniya musamman malaman addini da masoya manzon Allah SAW

Wane fata zaku yi mata?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Fatana da ita shine Allah Yayi mata kyakkyawan karshe. Na biyu shine ta sadu da Aisha El-Rufai ta koyar da ita matsayin manzon Allah a Musulunci da hanyoyin kare martabarsa da kuma iya baki wajen magana akan abinda mutum bashi da koshin ilimi a kai. Wassalam

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button