Labarai

JAMB ta ƙara kuɗin hidimar zana UTME zuwa N2,000

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire ta JAMB, ta umarci amintattun zana jarrabawar ta na’ura mai kwakwalwa, wato CBT, da su ƙara wa masu zana jarabawar kuɗin hidimar da su ke yi musu da ga naira 1,400 zuwa naira 2,000.

Hukumar JAMB ta bayyana haka a yau Litinin a cikin mujallarta ta mako-mako da ofishin magatakardar hukumar ke fitar waa Abuja. jaridar Daily Nigerian na ruwaito

Hukumar ta bayyana cewa da farko dai ƴan ɗaliban sun biya N1,400 wanda ya kunshi N700 na gwajin jarrabawar, wato mock-UTME da kuma wata N700 ɗin ta cikakkiyar jarrabawar ta UTME.

Hukumar ta ce matakin amincewa da hukumomin ta ya biyo bayan tsadar man dizal da sauran kalubalen makamashi a kasar.

“Daga yanzu, cibiyoyin CBT da mu ke da haɗin gwiwa za su karɓi jimillar Naira 2,000 a matsayin kuɗin hidima daga waɗanda suka yi jarrabawar gama sakandare (UTME) da kuma ta gwaji.

“Amma kuma ɗaliban da basu cike zana jarabawar gwaji ba, za su biya N1,000 ke kacal ma na UTME ɗin yayin da masu son zana jarabawar ta gwaji za su biya karin N1000.

“Wannan ba tare da la’akari da ko sun zauna jarrabawar ko basu zauna ba,” in ji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button