Labarai

IPOB sun kashe mai juna-biyu da ƴaƴanta 4 da wasu ƴan Arewa 6 a Anambra

Ƴan haramtacciyar ƙungiyar ƴan ta’adda ta IPOB, a ranar Lahadi sun kashe ƴan Arewa 10.

Mutane goman da ƴan IPOB ɗin su ka kashe sun haɗa da wata mata mai juna-biyu, ƴaƴanta huɗu da wasu mutane shida a Isulo, Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa a Jihar Daily Nigerian na ruwaito

An bayyana sunan matar da aka kashe da Harira Jibril, mai shekaru 32, yayin da yaran hudu kuma aka bayyana sunayensu da Fatima mai shekaru 9; Khadijah, 7; Hadiza, 5 da; Zaituna, 2.

Da yake bayyana yadda aka kashe matar tare da ‘ya’yanta, mijinta Jibril Ahmed ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun yi garkuwa da su ne a hanyarsu ta komawa gida bayan wata ziyara da suka kai Orumba ta Arewa.

Usman Abdullahi, shugaban al’ummar Hausawa a Ihiala shi ma ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce matar da aka kashe ‘yar asalin jihar Adamawa ce.

Ya ce daukacin al’ummar Hausawa sun bar Ihiala, sakamakon hare-haren da ake kai wa wadanda ba ƴan asalin yankin ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button