Labarai

Idan Atiku bai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba ka zabga min mari a duk inda muka haɗu -Reno Omokri

Wani tauraro ɗan Najeriya, marubuci kuma tsohon mai taimawa shugaban kasar Najeriya, mai suna Reno Omokri, ya mayar da martani a yanar gizo, yan mintuna da su ka wuce, domin bayar da amsa ga wani mai amfani da shafin Twitter, wanda ya taɓa ce masa, idan Atiku Abubakar ya fadi zaɓen 2023, to mutumin zai tuhumi Reno din ne da alhakin faduwar Atiku. LH na ruwaito

Reno Omokri ya mayar da martani

Da yake mayar da martani, ga wancan mai magana na Twitter, Reno ya bayyana kwarin gwuiwar sa akan Atiku, inda ya ce Atikun ne zai lashe zaben Shugaban kasar Najeriya na shekarar 2023, kuma idan har ya fadi, to wancan mai amfani da Twitter ɗin ya zabga masa mari a duk inda su kayi ido huɗu.

Kwarin gwuiwar da Reno yake da shi akan Atikun, wanda ya zama dan takarar Shugaban kasa na jamiyyar PDP a zaben shekarar 2023, ya burge mutane da yawa a dandalin na tuwita, inda suka raja’a akan sakon nasa.

Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fidda gwani

Idan dai zaku iya tunawa, Atiku Abubakai dai ya zama ɗan takarar jam’iyyar PDP na shugaban ƙasa ne, tun bayan da aka yi zaben fidda gwani na jam’iyyar ta PDP, inda ya sami kaso mai rinjaye na kuri’un da aka kaɗa, a wajen zaben fidda gwanin.

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya taka mahimmiyar rawa wajen samun nasarar Atiku, sakamakon janye takarar sa da yayi ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button