Labarai

Hukumar yan sanda ta ƙasa ta fitar da sunayen wadanda sunkayi nasara da ranar fara Medical screening

Rundunar yan sanda ta ƙasa sun fitar da sanarwa a shafin na sada zumunta cewa waɗanda sunka nemi aikin kurtu na yan sanda cewa an fitar da sunanyen wadanda sunkayi nasarar cin jarabawar kwamfuta ta CBT.

Wanda zaku iya amfani da shafin su domin duba wanda sunkayi nasara ga link da zakuyi amfani da shi wajen dubawa.

https://www.policerecruitment.gov.ng/#/status/nin/medical

Za’a yi wannan tantance lafiya mutum a turance “medical check up” a wuraren da za’a gudanar da wannan aiki a wurare goma sha bakwai 17 zone a fadin ƙasar nan.

Za’a fara wannan tantance lafiya daga 17 ga wannan watan mayu zuwa 31 ga watan nan.

Duk wanda zaije waje dole ya tafi da ƙaramar riga fara da guntun wando.

Abubuwan da ake bukatar kowa yaje da su a wajen:-

1- takarda shedar zama dan kasa

2- asalin takardun makaranta da kuma foto kwafi na takardunka na makarantar sikandiri.

3- takarda haihuwa “certificate of birth”

4- takardar shaidar haihuwar ta kotu “certificate/declaration of age”

5- ka shirya takardunka a cikin file farare gudu biyu da ƙaramin hoto “Passport photograhs ka zo da su.

6- sai kuma takardun da ka nemi aikin ka tabbatar da kaje da printout dinsu da kuma shafin wanda ya tsaya masa “Guarantors forms”

Duk wanda ya kuskura bai da abinda ake nema ba daga na farko zuwa na karsha to baza’a kula kaba a wajen tantancewa ba.

Wannan tantancewar kyauta ne ko sisi ba’a biya.

Allah ya bada Nasara Amen.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button