Addini

Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi – Malam Kabiru Gombe

Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa’azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhammad ﷺ ne jama’a su taru su kashe wani don sun ji ya zagi Annabi ﷺ

Malamin yayi wannan tsokaci ne a yayin da ya ke amsa tambayoyi daga Zuma Times Hausa a ofishinsa a Abuja inda ya jaddada cewa rashin sanin addini ne ya ke kawo irin waɗannan ɗabi’u a al’umma.

“Babban abinda ke jawo irin wannan shine jahilci, duk lokacin da al’umma ta zauna cikin jahilci kuma ga ta tana son addini, babu abin tashin hankali kamar mutum yana son Musulinci amma kuma bai san Musulunci ba, ko wani irin shirme zai iya yi da sunan Musulunci wanda hakan ya haifo mana da matsaloli da dama a Musulunci kuma har yanzun muna fuskantar wannan matsalar.”

Malam Kabiru Gombe ya ƙara da cewa ilimi ne kaɗai zai iya sa Musulmi su gane cewa, ba su ke da ikon yanke hukunci tare da zartar da hukunci ga mai laifi ba face hukuma.

“Addinin Musulunci bai yarda mutane su ɗauki doka a hannunsu ba ko da dokar ta Allah ce. Duk wanda ya yi haka ya saɓa wa Allah da Annabi Muhammaduﷺ .

“Hukama ita kaɗai aka yarda ta yi hukunci sannan ko hukumar ma akwai sharuɗa da aka gindaya kafin ta ɗauki hukunci ko ta zartar, milali, ta yi bincike sosai sannan a samu shaidu da sauransu kafin alƙali ya yanke hukunci sannan a zartar da wannan hukunci.

“Ba wai kawai da an ce wannan ya zagi Annabi sai a kashe shi, to ko da mutum ya ji ba shi ke da hurumin ya yanke hunkunci sannan ya zartar da hukuncin a Musulunci ba. Kai dai naka shaida ne ko ka yi ƙararsa ga hukuma. Misali in mutum ya yi sata an ce a yanke hannunsa ko in yayi zina a jefe shi amma ai ba Allah Ya ce ni da ku za mu zartar da wannan hukunci ba sai alƙali kuma dole sai an yin bincike da sheidu kafin a yanke hukunci.

“Ko a gabanka aka zagi Annabi ﷺ baka da hurumin zartar da hukunci sai hukuma in hukumar ba ta ɗauki mataki ba, babu ruwanka, ita Allah zai tambaya ranar Alƙiyama ba kai ba.”

-Zuma Times Hausa 2016

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. PLEASE WE DISAGREE WITH THE INFO ABOUT KABIRU GOMBE utrance send the audio on air the info isnt true

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button