Kannywood

Halin da Safara’u ta samu kanta iri daya ne da halin da miliyoyin Matasan Arewa maza da mata suke ciki – Dr Musa Abdullahi sufi

Ya kamata duk mai hankali ya kalli unguwar su da yan uwan sa wajen tabbatar da bada gudummawa wajen taimakawa matasa gane muhimmancin rayuwar gaba da illar biye wa jin dadi da rudanin yanzu.

Na kasance ina tattaunawa da matasa maza da mata masu harkar shaye shaye da saduwa barkatai bata auratayya ba yawanci Abin suna koya ne daga gida.

Malaman addini Kuma ku kara karatun lamarin nan don wasu masu aibata su kara kara Janyo habbaka lamarin suke.

Iyaye, mu gane mu ne shugabannin kasar gidajen mu, kuma Allah zai tambaye mu wannan amanar da ya bamu.

Hakika malamai da gwamnati su gudummawa ce tasu ga samar da damarmaki da zai sa matasan samu abinyi da kuma ilimi.

Mutuwar aure da rashin zaman lafiyar auren na taimakawa wajen tabarbarewar tarbiyyar matasan tun suna kanana.

Yan uwa da al’umma mu rike amanar marayu da taimakawa marasa karfi da hanyoyin dogaro da kai.

Amma batu na Gaskiya mu rike amanar juna, mu bar bakin ciki da hassada a tsakanin mu. Mu daina aibata Juna mu yawaita addu’ar shiriya ga kan mu da matasan mu.

Lokaci yayi da zamu kara tunani da kawo hanyoyin na ci gaba da bawa kungiyoyi da shugabanni shawarwari yadda za’a samu al’umma nagartacciya.

Duk wani mai neman kujerar mulki da bashi da tsarin inganta al’umma musamman matasa na tsarin zamani ba irin alkawarurruka yaudara ba.

Danmajalisa misali wadanne irin dokoki zai bijiro da su don kawo karshen wannan lamari.

Gidajen jaridu da telabijin masu shirye shirye yana da kyau su kawo shirye shiryen da zasu zaburar da matasa wajen hangen nesa, neman na Kai da sauran su.

Safara’u da duk kan mu Allah ya kara shiryar mu ya sa mu zama sanadin inganta Rayuwar al’umma.

Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button