Labarai

Ganduje ya zabi mataimakin sa Nasir Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi

Gwamnan jihar Kano dake Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya zabi mataimakin sa Nasir Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi a zaben shekara mai zuwa.

Bayanan dake fitowa daga Jihar sun ce Ganduje ya zabi Gawuna ne wajen taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC da aka gudanar a Jihar dangane da zaben mai zuwa. rfihausa na ruwaito

Mahalarta taron sun kuma amince da tsohon kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a matsayin wanda zai marawa Gawuna baya a zaben mai zuwa.

Majiyoyi daga wajen taron sun ce sanda jiga jigan jam’iyyar suka taka rawa sosai wajen sanya Garo janyewa daga neman takarar gwamnan domin komawa mataimakin Gawuna.

Masu sanya ido akan siyasar Kano sun ce Gawuna ya taka rawa sosai wajen ci gaban da jihar ta samu a bangaren noma da samar da abinci tare da goyawa Ganduje baya wajen jagorancin jihar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button