Labarai

Firaministan Sri Lanka ya sauka saboda zanga-zangar ƙin gwamnati da kuma tsadar rayuwa

Hukumomin Sri Lanka sun ce firaministan kasar, Mahinda Rajapaksa, ya sauka daga mukaminsa sakamakon zanga-zangar kin gwamnati ta gama-gari da ake yi da kuma tsadar rayuwa.bbchausa na ruwaito

Mista Rajapaksa, ya ajiye aiki ne yayin da aka sanya dokar hana zirga-zirga bayan mummunan tashin hankalin da aka samu tsakanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma masu goyon bayan firaministan da dan uwansa, Shugaba Gotabaya Rajapaksa.

Rahotanni daga wani asibiti a babban birnin kasar Colombo, sun nuna cewa an jikkata akalla mutum 78 a tashin hankalin da aka gwabza a wajen fadar shugaban kasar.

Dubbai sun kaurace wa karbar maganin cutar kanjamau a Mozambique

Hukumomi a Mozambique sun ce masu dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki sama da dubu 14 sun daina zuwa karbar maganin rage kaifin cutar a watanni uku na farkon shekara a lardin Zambézia na tsakiyar kasar.

Shugabar shirin yaki da cutar a yankin, Dr Cheinaze Veríssimo, ta ce, yawancin wadanda suka daina zuwa karbar maganin maza ne.

Ya dora alhakin yawan kauracewar a kan tsangwama da kyama da ake nuna wa masu cutar.

Sama da mutane dubu 300,ne ke karbar maganin rage kaifin cutar da AIDS ko SIDA a lardin na Zambézia.

Likitan ya ce matsalar da suke fuskanta ita ce, idan mutum ya daina shan maganin, bayan ya fara, hakan zai sa kwayar cutar ta kara karfi, abin da zai iya sa mutum ya kamu da rashin lafiya sosai har ma a wni lokaci abin ya kai ga rasuwa.

Dr Veríssimo ya ce yanzu jami’an lafiya za su rika kai maganin har gida ga jama’a, ga wadanda ba za su iya zuwa asibiti ba, saboda rashin lafiyar ko kuma gudun tsangwama.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button