LabaraiToturials

Dalilin Da yasa ba’a sako sakamakon jarabawar JAMB UTME na wasu daga cikin ɗalibai

Tun bayan da hukumar JAMB ta saki sakamakon Jarrabawar UTME ta wannan shekarar, a ranar Asabar ɗin da ta gabata, mun samu ƙorafe-ƙorafe da dama na rashin sakin sakamakon Jarrabawar wasu daga cikin ɗaliban, yayin da wasu kuwa hukumar ta JAMB ta gaza bayyana musu halin da sakamakon Jarrabawar tasu yake a ciki ma baki ɗaya.

Sai dai, hukumar ta JAMB ta bayyana dalilan da suka sanya ta riƙe sakamakon Jarrabawar irin waɗannan Ɗalibai, a zantawar mai magana da yawun hukumar, Dr Fabian Benjamin, da jaridar PUNCH a yau.

Daga cikin dalilan da hukumar ta bayyana na gaza sakin sakamakon Jarrabawar, sun haɗar da :

• Zargin satar amsa, a yayin rubuta jarrabawar.

• Nuna rashin tarbiyya, ko sa’insa da wakilan hukumar da JAMB ta turo, domin sanya ido a cibiyoyin rubuta jarrabawar.

• Karyawa, ko rashin bin tsare-tsaren da hukumar ta gindaya a cibiyoyin rubuta jarrabawa.

• Sai kuma dalili na ƙarshe, wanda shi ne; rashin kammala tantance jarrabawar wasu cibiyoyin da hukumar JAMB ta ke cigaba da yi.

Abin lura : Za’a saki sakamakon Jarrabawar Ɗaliban da ba’a kammala tantance jarrabawar cibiyoyin su ba, da zarar hukumar ta kammala.

Haka zalika, Ɗaliban da ake zargi da satar amsa ma, za’a saki nasu sakamakon, da zarar hukumar ta kammala tantancewa tare da tabbatar da cewar basu aikata laifin da take zargin su da shi na satar amsa ba, yayin da kuma hukumar zata soke sakamakon Jarrabawar Ɗaliban da ta samu dumu-dumu da satar amsa a yayin jarrabawar.

✍️Miftahu Ahmad Panda.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button