Labarai

Daga Taimako, ’Yar Ukraine Ta ‘Kwace’ Mijin ’Yar Birtaniyar Da Ta Ba Ta Masauki

Wata ’yar Birtaniya ta bayyana da-na-saninta kan yadda ta ce abin arziki ya zama na tsiya, bayan wata ’yar kasar Ukraine ta kwace mata miji, kwana 10 baya ta sauketa a matsayin ’yar gudun hijira.

Matar mai suna Lorna Garnett, wacce ke zaune a birnin Bradford na Birtaniya dai ta zargi mijin nata mai suna Tony da yin watsi da ita, inda ya bi budurwar ’yar Ukraine mai shekara 22.Aminiya na ruwaito

Jaridar Sun ta Birtaniya ta rawaito cewa Lorna, mai shekara 28 wacce take da ’ya’ya uku ta shiga matukar damuwa bayan mijin nata ya tsallake aurensu mai shekara 10, sannan ya bi Sofiia Karkadym, ’yar gudun hijirar da ta ba mafaka.

Sun dai ba budurwar mafaka ne bayan ta gudo daga kasarta, sakamakon yakin da Ukraine ke gwabzawa da Rasha.https://aminiya.dailytrust.com/daga-taimako-yar-ukraine-ta-kwace-mijin-yar-birtaniyar-da-ta-ba-ta-masauki

Matar ta ce, “Tun farko sai da na yi kaffa-kaffa kan ba ’yar gudun hijirar masauki a cikin gidanmu, amma waye ba zai yi haka ba?

“Mun kawo matar da ba mu sani ba ta rayu da mu a cikin gidanmu. ’Yan Ukraine na cikin mawuyacin hali, sai na fahimci ba karamin taimako ba ne ka ba mutum masauki saboda yana tsananin bukata.

“Amma wannan shi ne abin da Sofiia za ta biya ni da shi bayan na rufa mata asiri,” inji Lorna.

Tony Garnett dai ya amince ya ba budurwar masauki ne bayan sun fara haduwa a dandalin sada zumunta na Facebook.

Sofiia dai wacce kwararriya ce a harkar na’ura mai kwakwalwa na zaune ne a Kyiv, babban birnin kasar ta Ukraine, kuma an ba ta izinin shiga Britaniya ne a farkon watan Mayu.

Sai dai ’yan kwanaki bayan ta zo gidan nasu, sai Sofiia ta fara dasawa da mijin Lorna, lamarin da ya sa ta fara da-na-sanin ba ta mafakar tun da farko.

Bayan ta fahimci yadda shakuwarsu ta dada karfi ne Lorna ta bukaci Sofiia ta bar musu gida.

Sai dai ta shiga matsananciyar damuwa ce bayan mijin nata shi ma ya kwashe kayansa ya bi ’yar gudun hijirar.

Daga bisani dai mijin ya shaida mata cewa yanzu ya fada kogin soyayya da ’yar gudun hijirar Ukraine din.

Sai dai bayan bazuwar labarin a kasashen Birtaniya da Ukraine, iyayen Tony sun fatattake su daga gidansu da suka je suka fake a ciki.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button