Birtaniya: Bayan shekaru wasu musulmai na sallah a bandaki, an samar musu da wuri na musamman
Wata makarantar sakandiri a Derby, dake Birtaniya ta siya dadduman sallah tare da samar da kebabban wurin sallah don ba wa dalibai musulmai damar sallah cikin natsuwa bayan shugaban malam ta gano yadda aka tilasta su yin salloli biyar dinsu a ban dakin makaranta saboda babu wurin yin sallah, Daily Trust ta ruwaito.
Michelle Strong, shugabar malaman makarantar Alvaston Moor, ta ce ta yanke shawarar siyan akwatina biyu na dadduman sallan ne bayan gano hakan, sannan ta shiryawa dalibai musulman don suyi amfani dashi a wajen ma’adanar littafai da rana, inda aka kebance musu wuri. Wani lokaci idan ana amfani da ma’adanar littafan, ana nema ma daliban wani daki daban don suyi sallah cikin kwanciyar hankali.
Mrs Strong, wacce ita ce ke kula da lamurran dalibai 850 na makarantar Alvaston Moor a watan Satumba 2021, ta ce:
“Mun siyo wadannan dadduman sallan ne saboda yana da mahimmaci kula da duk wata al’ada. Muna cikin makarantar hadaka. Akwai bukatar mu gane duk wata al’ada da yaranmu ke da ita a wannan makarantar. Tunda muna shagalin bikin kirsimeti shima.
“Ya kamata makarantu su zama wani mara damuwa inda kowa ke da damar yin rayuwarshi da bayyana addininsa idan yana son yin hakan.
“A halin yanzu, dalibanmu musulmai na da sabbin dadduman sallan su. Ina fatan hakan yasa sunji a dauke su da kima kuma an mutuntasu, sannan mutane suna gane addininsu.”
Ruhaan Rizwan, wanda ke cikin shekara ta 8 a Alvaston Moor, na daya daga cikin daliban dake amfani da dadduman sallan da rana.
LH ta raƙa da cewa Ruhaan yayi godiya ga Mrs Strong da mai kula da ma’adanar littafan Brackens Lane, Amber Fletcher a kan yadda ta siyo dadduman sallan sannan aka kebance wani wuri da ma’adanar littafan makarantar don dalibai musulmai suyi amfani dasu wurin yin sallah.
A cewarsa: “Mrs Strong da Miss Fletcher sun dade suna nuna halin dattaku. Naji dadin hakan matuka. Ina tunanin wannan makarantar na da dattaku. Ina matukar godiya ga hakan. Bazan iya misalta irin tsananin farincikin da na shiga ba.”