Labarai

Bidiyon uban angon da ya bude fili da rawa a liyafar auren dansa

Wani bidiyon da shafin Arewafamilyweddings su ka sanya a ranar Lahadi ya dauki hankalin jama’a matuka.

Kamar yadda aka gani a bidiyon, uban ango ne ya bude fili da rawa yayin shiga wurin liyafar auren dansa.

Mutumin, kamar yadda shafin da ya wallafa ya bayyana, mahaifin ango ne wanda ya bayyana farincikinsa karara akan auren dansa.

Kuma alamu na nuna cewa dan arewa ne kasancewar sutturar da ke jikinsa babbar riga ce da kuma hula kube, sannan ko yanayin suffarsa ma ta mutanen arewa ne.

Wannan ba abu ba ne da aka saba da shi a arewa ba. Saboda akwai iyayen da su ke ganin rashin dacewar yara su shirya liyafa yayin aurensu, har wasu su kan hana.jaridar LH

Akwai iyayen da su ke bari a shirya liyafar sai dai ba sa zuwa. Akwai kuma wadanda su ke zuwa amma ba sa taka rawa duk da su na wurin.

Akan samu iyayen da ke taka rawa musamman mata, amma yana matukar wahala a ga mahaifin ango dakanshi yana kwasar rawa a bainar jama’a.

Wannan ya sanya bidiyon ya dauki hankali don ko karkashin shi sai da LabarunHausa.com ta hango tsokacin mutane.

Wasu sun nuna cewa ba komai ba ne, hasali ma ya burgesu. Amma wasu kuma sun caccake shi, inda su ke cewa bai dace da dabi’ar dan arewa ba.

Ga bidiyon:

 

Tsokacin jama’a a karkashin bidiyon

halima_gj ta ce:

“Ana bariki a duniya.”

fatimainuwa28 ta ce da turanci:

“Idan amaryar diyata ce, zan iya fasa bayar da auren.”

aliyu_bakura ya ce:

“Tsohon bariki.”

darkestgostt ya ce:

“Kuna son yanke wa mutane hukunci. Menene don ya yi rawa a ranar auren dansa? Ko kuna bakinciki ne? Kawai ba kwa son mutum ya yi farinciki? Ya kamata su kwantar da hankalinku. Haba!.”

ihsaan_j ta ce:

“Mutumin nan ya burgeni. Akalla ya cire kunya ya mori auren dansa.”

azeez_abdul ya ce:

“Allah wadaran naka ya lalace. Kash! An dai ji kunya Wallahi.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button