Labarai

Bam ya kashe ƴan Boko Haram 6 a Borno

Ƴan ƙungiyar Boko Haram/ISWAP ne su ka mutu a wani tashin bam da su ka dasa domin ya tashi da sojoji a Jihar Borno.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa majiyoyin tsaro sun baiyana cewa ƴan ta’addan sun gamu da ajalin su ne a ranar Alhamis, a kan hanyar su ta dawowa da ga kai hare-hare a kan hanyar ƙauyen Nguma da ke Ƙaramar Hukumar Biu.

Majiyoyin sun ce ƴan ta’addan sun taho a motoci Masu ɗaukar jigida guda 3 da babura ɗaya a hanyar su ta dawowa da ga Sabongari da Multe, sai mota ɗaya ta taka bam ɗin.

Nan take bam din ya kashe shida daga cikin su inda saura kuma su ka ji muggan raunuka.

Rahotannin sun ce ƴan ta’addan da su ka rayu sun huce haushin su a kan wani bafilatani, inda su ka kashe shi da matar sa da kuma ɗan sa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button