Ba zan iya biyan Delegate ko sisi ba domin ya zabeni – Cmrd shehu sani
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP Comrade Shehu Sani ya ce ba zai biya wani delegate ko sisin kwabo ba domin ya zabeshi.Mikiya na ruwaito.
Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace “Zaben Firamare na Gwamnonin Kaduna Ba zan biya kowane delegate su zabe ni ba, kuma babu wanda ya isa na biya shi domin a zabe ni, ina maraba da kuri’a bisa manufata ta al’ummar jihar Kaduna, ba za mu iya gina kasarmu ba, ba za mu ci gaba ba ta hanyar rashin gaskiya a tsarin daukar ma’aikata jagoranci.”
Comrade Shehu Sani na daya daga cikin wadanda za su fafata a zaben fidda gwani na gwamnoni a jam’iyyar PDP.
Saidai kuma jama’a da yawa na ganin indai Shehu Sani ya tafi akan wannan matsayar tashi, to kuwa la shakka zai ci kasa. Lokaci ne zai yi alkalanci.