Labarai

Ashe Ba Dillalin Motoci Bane Mai Wanke Mota Ne-Inji Wata Amarya Data Gano Aikin Mijinta Bayan Aurensu

Maza da daman gaske suna shigowa da yaudara a harkar neman aurensu. Wanda hakan ma yana daya daga cikin matsalolin da suke jawo mutuwar aure.
Su kuma mata da zaran sun ga namiji yana dan haskawa, shi kenan babu ruwansu da ganon gaskiyar aikinsa ko sana’ar sa.

Su kuma iyaye ko wakilan matan da aka zo neman auren nasu, basu damu su tsananta bincike akan wanda zai auri wata nasu ba burinsu kawai tayi aure ta bar musu gida idan taga dama gobe a sakota ta dawo.

Yanzu haka dai wani auren da akayi watannin uku da suka wuce a garin Abuja yana neman rasuwa. Domin amaryar watannin 3 ta gano ainihin aikin da mijinta ya keyi sabanin sana’ar daya nemi aurenta dashi.

“A lokacinda yazo neman aurena naga yana zuwa da Motoci na garari daban daban. Na tambayeshi sana’ar sa sai yace mini shi dilan Motoci ne. Ya kuma fadamini inda ofis dinsu yake. Bayan nayi tambaya aka tambayar mini anan yake aiki amma ban san wankin motoci yake yi ba a nan ofis din nasu sai bayan da mukayi aure wani abu ya kama naje can ba shiri na sameshi a tsakiyar Motoci yana wankesu”. Inji Amaryar watanni 3.

Sai dai ta kara da cewa,” a gaskiya ina sonshi, koda tun farko yace mini wankin mota yake yi zan iya aurensa a hakan. Domin na soma fahintar akwai karya a Lamuransa ne tun bayan da aka soma hidimar auren da kuma inda zan zauna. Sai dai hakan bai sa nayi magana ba. Kuma dai-dai gwargwado tunda mukayi aure yana kula dani bana kuma zarginsa da komai. Amma tunda na fahimci karyar sana’a dana wasu abubuwan da yamini a baya kawai sai zuciyata ta kasa natsuwa da shi. Saboda bazan iya tabbatar da gaskiyar sa nan gaba ba”.

Inda ta nemi da wannan shafin Tsangayarmalamtonga ya nema mata ra’ayin mutane su bata Sha’awaran abunda ya kamata tayi. Inda tace tunda abun ya faru mijin nata ya daina ganin walwalarta shi kuma ya kasa fitowa fili ya yarda shi Dan wankin mota ne.

Da fatan masu karatu zasu bata shawaran daya dace.

Daga : Tonga Abdul tonga

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button