Labarai

APC na zaizaye wa a Kano bayan da Shekarau, Rurum da Kawu Sumaila ke shirin koma wa NNPP

Jam’iyar APC na fuskantar ficewar wasu jiga-jigan ta a Jihar Kano yayin da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ɗan majalisar taraiya mai wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya, Alhassan Rurum da kuma tsohon ɗan majalisar wakilai, Kawu Sumaila su ka kammala shirye-shiryen sauya sheƙa zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP.

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa Shekarau ɗin ya kira taron manyan mashawartansa a siyasa, wanda aka yi wa laƙabi da ‘Shura Council’, inda zai bayyana sauya sheƙar ta sa a yau Talata.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa Rurum da Sumaila, waɗanda jiga-jigan ‘yan siyasa ne a yankin Kano ta Kudu, sun gana da jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso, a Abuja jiya Litinin.

Baya ga ’yan majalisar wakilai tara na PDP da su ka koma NNPP, tuni wasu jiga-jigan ’yan siyasar APC guda biyu a Kano ta Arewa, Tijjani Jobe (mai wakiltar mazabar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimin Gado Federal Constituency) da Mohammed Butubutu (mai wakiltar mazabar tarayya). Mazabar Rimin Gado/Tofa a majalisar dokokin Kano) sun fice daga APC ɗin zuwa NNPP.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa DAILY NIGERIAN cewa “Mallam Shekarau shima yana tuntubar shugabannin NNPP kuma ya kammala shirin barin APC ya koma NNPP ɗin tare da Haruna Dederi da Nasiru Auduwa, mambobi masu wakiltar mazabun Karaye/Rogo da kuma Gabasawa/Gezawa.

Uwar jam’iyya ta ƙasa ce ta sulhunta Shekarau, wanda bangarensa ya sha kaye a rikicin shugabanci a kotun koli a makon jiya da Gwamna Abdullahi Ganduje.

Amma kuma sulhun bai yi ƙarko ba sabo da rashin tabbaci da amince wa na tsayar da Shekarau ɗin a matsayin ɗan takara, kamar yadda majiyoyin su ka baiyana.

Kamar yadda wata yarjejeniya da ba rubutacciya ba da uwar jam’iyar ta gudanar, jam’iyar, a ko wacce jiha, za ta baiwa tsoffi da gwamnoni masu ci tikitin takarar Sanata kai tsaye.

Amma majiyoyin sun baiyana cewa shi Shekarau bai amince da haka ba duba da cewa akwai wasu ƴan takara da tuni suka sayi fom ɗin takara domin kara wa da shi a zaɓen fidda-gwani.

Tuni dai Bashir Garba Lado, A.A. Zaura da Ismail Ahmed su ka sayi fom ɗin takarar Sanata a Kano ta tsakiya domin fafata wa da Shekarau.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button