Labarai

Ana Dab Da Fara Kurɓar DATA Kyauta A Najeriya

Albishirinku ‘Yan Najeriya  ga wani sabon labari na farin ciki, kasancewar a yanzu rayuwa ta kasance sai da hanyar sadarwar ta zamani sannan kuma sadarwar kowa yasan na buƙatar mahaɗi wato Data wace ke bada damar shiga yanar gizo-gizo.

Attajirin nan Elon Musk dake ƙasar Amurka ya lashi takobin kawo ƙarshen matsalar Data a Nan Najeriya wadda ta daɗe tana sanya dubban mutane rashin farin ciki a yayin amfani da yanar gizo-gizo.

Mai kuɗin duniyar dai ya sami lasisin sahalewa daga hukumar NCC wace take kula da dukkan abubuwan da suka shafi sadarwar zamani.

Kamfanin attajirin mai suna Starlink ya duƙufufa wajen shawo kan matsalar ta Data wanda a iya yanzu aikin yayi nisa

Kamfanin zai zama kishiya ga sauran kamfanonin da muke dasu nan nan gida inda ‘yan ƙasa ke dakon ganin wannan lamari yafara aiki domin zaɓar dokin da zai kaisu izuwa filin daga cikin hanzari  ba wanda zai watsar dasu ba a tsakiyar sahara!  Muna fata wannan kamfani yazama ya share hawayen ‘yan Najeriya da Data mai inganci da kuma rangwame domin kawar dukkan na’uin ‘yan Free Mode dake danƙare a social media.

Kamfanin zai zama kishiya ga sauran kamfanonin da muke dasu nan nan gida inda ‘yan ƙasa ke dakon ganin wannan lamari yafara aiki domin zaɓar dokin da zai kaisu izuwa filin daga cikin hanzari  ba wanda zai watsar dasu ba a tsakiyar sahara!

Muna fata wannan kamfani yazama ya share hawayen ‘yan Najeriya da Data mai inganci da kuma rangwame domin kawar dukkan na’uin ‘yan Free Mode dake danƙare a social media.

Sources :arewatalent

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button