Labarai

An yanke wa wani rago hukuncin shekara 3 a gidan kaso bisa halaka wata tsohuwa

An yanke wa wani rago hukuncin shekara 3 a gidan kaso bayan ya halaka wata mata a sanadiyyar tunkuyin ta.LH ta wallafa

Shafin LIB ya rahoto cewa ragon ya hari matar mai suna Adhieu Chaping, mai shekaru 45, inda ya tunkure ta sau da dama a ƙirji kafin ta rasu a ƙarshen mako.

An bayyana yadda hukuncin zai kasance

Daga cikin hukuncin, ragon zai kwashi wani lokaci a tsare a wani sansanin sojoji bayan shugabannin gargajiya sun masa hukunci a ƙasar Sudan ta kudu.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan’uwan matar an sanar musu da cewa mai ragon zai basu shanu 5 a matsayin diyya.

Ragon ya kai mata hari ta hanyar tunkurin ta a haƙarƙari inda nan take tsohuwar ta mutu.

Jam’in ɗan sanda Elijah Mabor ya shaidawa gidan rediyon Sudan’s Eye

Wannan shine abinda ya faru a Rumbek East a wani wuri da ake kira  Akuel Yol.

Aikin mu a matsayin ‘yan sanda samar da tsaro da kuma rabon faɗa. An kamo ragon inda yanzu haka hannun mu a ofishin ‘yan sanda na Maleng Agok Payam

Zaa bayar da diyyar kisan da ragon yayi

Hukumomi sun tabbatar da cewa iyalan biyu sun amince cewa mai ragon zai bayar da shanu 5 biss yarjejeniƴar da aka cimmawa da shugabannin ƙauyen.

An bayyana sunan mutumin da yake da ragon a matsayin Duony Manyang Dhal.

Za a bayar da ragon kyauta ga iyalan Chaping da zarar an sako shi daga gidan kaso, bisa tanadin doka.

Sai da iyalan biyu su ka sanya hannu akan yarjejeniyar domin tabbatar da ita inda shugabannin garjajiya su ka zama shaidu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button