Labarai

An Tsinci Gawar Wata Zukekiyar Budurwa, Bayan Ta Kama Dakin Otal Da Gungun Samari

Advertisment

Wata budurwa mai shekaru kusan 30, mai suna Ugochi Nworie ta rasa rayuwarta sanadiyyar hadaka wurin yi ma ta fyade a wani Otel cikin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi da wasu samari suka yi.

An gano yadda wacce lamarin ya auku da ita ta isa Otel din tare da wasu maza a duhun dare, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Daga bisani aka tsinci gawar budurwar a dakin Otel din, bayan an balle kofar a ranar. An tarar da an daure ma ta kafafu, hannaye da baki.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Loveth Odah, wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ana kokarin ganin an zakulo wadanda suka tafka aika-aikar, sannan suka bar dakin Otel din ba tare da an gane ba.

An tsinci kwararon robobi da aka yi amfani dasu a dakin yayin bincikar shi da aka yi.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button