Sheikh musa Yusuf asadus sunnah yayi taƙaitaccen bayyani akan cewa a wajen rufe tafsirinsa yayi magana akan wani fusto da ‘ya’yansa su goma da mabiyansa sunkai mutum darin shidda wanda yace yana bibiyar shafin Naziru Sarkin waka yana ganin abubuwan da yake yi shiyasa zai musulunta shi da ƴaƴansa goma da mabiyansa sunka mutum dari shidda.
To duk wanda ya damu da addinin musulunci zaiji dadi irin yadda wadannan mutane zasu karbi Musulunci shine naziru Sarkin waka Allah ya saka masa da alkhairi.
To shine Naziru Sarkin waka yace zai dauki duk abinda za’a kashe akan karba addinin musulunci.
Wanda nan take ya nemi wani malami wanda yace a nemi malamai domin yadda za’a baiwa wannan fusto da mutanensa musulunci amma sarkin waka yacewa malam karku yadda ya kiraku kawai kuje domin ba’a san abinda ya shirya ba.
Wanda malam sunka dauki wannan shawara ta naziru Sarkin waka inda anka shirya karkashin wata Foundation ta musulunci.
Ga cikakken bayyanin nan daga bakin Sheikh musa Yusuf Asadus sunnah.