Kannywood

Abinda ya sa nake son Jarumi Rabi’u Rikadawa – Cewar Ladidi Tubless

Ladidi Tubless, dattijuwar jaruma a masana’antar Kannywood ta bayyana dalilin da ya sa take son jarumi Rabi’u Rikadawa, wanda aka fi sani da Dila ko kuma Baba Dan’audu, a wata tattaunawa da Aminiya ta yi da jarumar.

Kamar yadda ta bayyana, Rikadawa ne ya sanya mata suna Ladi Tubless wanda yanzu haka ta yi fice da shi a masana’antar Kannywood.

Ta ce kaddara ce ta kawo ta masana’antar musamman ganin cewa idan har Allah ya yi sai ka ci abinci a wuri to babu shakka hakan sai ya tabbata.

Abinda ya sa nake son Jarumi Rabi’u Rikadawa, Ladidi Tubless
Abinda ya sa nake son Jarumi Rabi’u Rikadawa, Ladidi Tubless

Ta bayyana yadda ta fara shirin fim tun daga makaranta lokacin ana hada ‘yan shirye-shirye har Ubangiji ya yi zata ci abinci da harkar.

Yayin da aka tambayeta fim din da tafi so, ta ce duk fina-finanta tana matukar son su musamman wadanda ta kashe kudadenta wurin shirya su da kuma wadanda aka nemi ta yi su saboda ta karu kuma tana matukar alfahari da su.

Ta kuma hori matasa na masana’antar da su kasance masu neman ilimi ko da kuwa ba neman aiki za su yi da shi ba saboda akwai lokacin da zai zo wanda in har babu ilimi ba za a yi da mutum ba.labarunhausa na tattara labarai.

An tambayeta namijin da ta fi so a masana’antar Kannywood inda ta kada baki ta ce:

“Wanda na fi so a cikin mazajen fim, Alhaji Rabi’u Rikadawa, Dila wato Baba Dan Audu. Ai shi kamar dan uwana ne, yayana ne, aboki na ne kuma duk muna tare.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button