Labarai

Abdulmalik Tanko ya yarda da sace hanifa amma ya karyata abun kashe ta

Abdulmalik Tanko, malamin makaranta da ake zargi da sace dalibarsa mai shekaru 5, Hanifa Abubakar, da kuma ya kashe ta, ya sake musanta batun sanin yadda aka yi yarinyar ta mutu.

Ya karyata batun ne a babbar kotu mai lamba ta 5, da ke zama a Audu Bako a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto. Legithausa.

Mai shari’a Usman Na’abba ne ya jagoranci zaman kotun. Tanko, wanda a baya ya amince da hada baki da wasu wajen aikata laifin, ya musanta sauran tuhume-tuhume uku da ake masa da su da suka hada da yin garkuwa da yarinyar da kuma kashe ta daga baya

Yayin da ya yarda cewa ya kai Hanifa makarantarsa sannan ya kulle ta, Tanko ya ce:

Ba ni da tabbacin ko ni ne mutum na karshe da ya ganta a raye saboda tun da farko na sanar da wani batun. Ban kashe ta ba haka kuma ban bata guba ba. Na bar ta tana barci ne sannan na dawo na gan ta a mace.

“Ni da wadanda ake tuhuma na biyu da uku bamu san yadda aka yi ta mutu ba.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button