Labarai

2023: NNPP ta zaɓi Kwankwaso a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa

Advertisment

Sabuwar jam’iyyar hamayya ta NNPP ta ayyana tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da za a yi a 2023.

Wannan ya nuna Kwankwaso zai tunkari ƴan takarar manyan jam’iyyun da su ka haɗa da APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

VOA ta rawaito cewa shugaban jam’iyyar NNPP Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali ya ce sun yi dogon nazari kafin tsayar da Kwankwaso don ya zama daidai da sauran manyan ƴan takara da za su fafata a zaben.

Ya ƙara da cewa Kwankwaso ne kaɗai ya sayi form ɗin takarar shugaban ƙasa a NNPP, inda ya ƙara da cewa duk da haka, za a haɗa taro domin ƙara jaddada shi da kuma kaɗa masa kuri’a a ranar zaɓen fidda-gwani.

Advertisment

Tuni wasu jam’iyyun su ka gudanar da zaben fitar gwani kamar PDP da ta zabi Atiku Abubakar, Labor ta tsayar da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi, inda APC za ta yi zabenta a ranar Litinin mai zuwa don shirin mika sunayen gwanaye ga hukumar zabe zuwa 9 ga watan Yunin nan.

Kwankwaso wanda a da mamba ne a jam’iyyar PDP da APC, ya ce ya yi wa dukkan ‘yan takarar farin sani kuma ba ya shakkar gamuwa da su ranar zabe.

Ya kara da cewa, NNPP za ta kawo wani tsarin da zai kawar da muradun ‘yan jari hujja a dimokrdaiyyar Najeriya.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button