Labarai

Ƙasar Saudiya Ta Cafke Ƴan Najeriya 20 Masu Ɗaga Hotunan Ƴan Siyasa A Ɗakin Ka’abah

A umrah bana abubuwan yan Nijeriya sunyi yawa sosai irin yadda sunka maida ka’aba wajen daukar bidiyo da hotuna saɓanin inda anka fito.

Inda yanzu lamarin ya chanza zane wanda har hotunan yan siyasa ake zuwa da su a masallacin domin tallata dan takara wanda abun yayi matukar muni ga abinda Arewa media ta kawo rahoto akai.

Hukumomi a ƙasar Saudiyya, sun cafke mutane 20, da aka kama su na daga Hotunan Bola Tinubu da sauran wasu Ƴan siyasan Najeriya a gaban ɗakin Ka’aba, a cewar hukumomin za a hukuntasu.

Majiyar ta cigaba da cewa a yanzu haka suna hannun mahukunta ƙasar, ƙarƙashin kulawar askarawa domin gurfanar dasu gaban kotu tare da yanke masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata, majiyar kuma ta cigaba da cewa babu shakka zasu kwashi kwashin su a hannu.

Majiyar mu ta kuma jiyo cewa, hukumomin sunce Sam baza su laminci ire-iren waɗannan abubuwan da ‘Ƴan Najeriya suke ba, domin yin wani abu na daban a cikin ƙasar su ba, domin kuwa wannan sabon wani abu ne dasu ba Susan da shi ba.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button