Labarai

Yanzu – Yanzu: Mun kori Nuru Khalid daga limancin Masallacin Apo gaba daya – Dan Sadau

Bayan dakatar da malam sheikh nuru Khalid da ankayi akan yayi huduba mai zafi wanda yayi akan matsalar rashin tsaro a juma’ar da ta gabata shine yanzu nan majiyarmu ta samu labari daga shafin Bbchausa sun ruwaito cewa.

Sanata Sa’idu Muhammad Dan Sadau shugaban kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen Yan Majalisar Najeriya na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ɗaya.

Sanata Dan Sadau ya shaida wa BBC Hausa cewa sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan.”

 

Wasiƙar ta ce: “Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi’ar mutum.

 

“Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka faɗa.

“Shugabanci na buƙatar sauke haƙƙi ka’in da na’in. Idan kalamanmu sun ɓata wa ƴan ƙasa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na ɗaukar matakin da ya dace saboda al’umma.

“Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara huɗubarka ta ranar Juma’a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya,” in ji sanarwar.

A hirarsa da BBC Sanata Dansadau ya ce “malamin ya nuna cewa ko da kwarar zarra bai yi nadama ba ga abubuwan da ya yi, don haka bisa haka ba mu iya zama da shi.

“Ibada ce ba ma iya bin shi Sallah, kuma nafsi ya yarda idan ba ka iya bin mutum Sallah kana da damar ka sake Masallaci,” in ji shi.

Sanatan ya ƙara da cewa “Masallaci wurin ibada ne, ba wurin sukar gwamnati ba ne.”

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button