Labarai

Yan bindiga na iya taɗa Najeriya baki ɗaya

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Nasir Ahmed El-Rufai ya ce ‘yan Boko Haram ne suka tsara tare da aiwatar da hari kan jirgin kasa a Abuja zuwa Kaduna a jiharsa.
Gwamna ya bayyana haka ne a wannan Juma’a lokacin da ya ke yiwa manema labarai bayani kan sakamakon ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa. Bbchausa na ruwaito
El-Rufai ya ce harin ya yi sanadi mutuwar aƙalla Fasinjoji takwas da raunatar wasu 40 da kuma garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.
Ya kuma shaida cewa an samu tattaunawa tsakanin iyalai da wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai har yanzu ‘yan bindigar ba su tambaye kuɗi ba, illa daga wajen mutum guda.
Amma gwamnan ya ce yana zargin watakil daga wajen gwmanatin za su neman diyya, ba daidaikun mutane ba ko iyalansu.

Harin wannan lokaci ya bambanta’
Gwamna El-Rufai ya ce ya shaidawa Shugaba Muhammadu Buhari cewa salon harin ‘yan bindigar na wannan lokaci ya bambanta da wanda aka saba gani a baya saboda ‘yan Boko Haram ne suka taimakawa ɓarayin dajin.
Sannan a halin da ake ciki yanzu jami’an tsaro na duba inda suke ɓuya domin yi musu kawanya don daukar matakan da suka dace.
Ya kuma ce; “A kullum gwamnati tana duba batun rayuwar mutane, don haka indai ba an fitar da mutanen da aka sace bane, ba za a iya wani abu ba a yanzu kamar kai musu farmaki“.
‘Ba ma biyan fansa’
El-Rufai ya ce su gwamnatin Kaduna ba sa biyan diyya ko kuɗin fansa don haka babu wannan batu a yanzu, ko a tattaunawarsu da shugaban kasa.

Gwamnan ya jadada cewa tun da fari sun aike da sakon gargaɗi zuwa ga hukumomin jirgin kasa cewa ‘yan Boko Haram sun shigo kuma suna tsara wannan hari.
Ya ce wannan ne dalilin da ya sa ya ce a takaita zirga-zirgar jirgin musamman in dai dare ya yi..
Mun sha rubuta wasika ga hukumar zirga-zirgar jirgin kasa da sanar da su cewa Boko Haram za su kai hari kan jirgin.
“Sannan jirgin sojin sama sun je katari sun yi sansani inda helikwafta zai iya sauka da shan mai saboda idan wani abu ya faru su gaggauta kai sauki.
“Sai dai da yake daddare ne hakan ya kasance da wahala. Kuma dama maharan sun shirya sosai sun san jirgin da suke son kai wa hari, suna da labarin manyan mutane da ke cikin jirgi.”

‘Yan bindiga na iya taɗa Najeriya baki ɗaya’
Gwamnan ya ce ya sake jadadawa shugaba Muhammadu Buhari matsayarsa na a ƙona dazuzzuka da waɗannan ‘yan ta’adda ke ɓuya baki ɗaya.
Ya shaida cewa wannan babban al’amari ne wanda ya kamata dazuzzuka da ‘yan tadda suke a sakar musu bam a kashe kowa, a cewarsa.

Na faɗawa shugaba Buhari Idan ba hakan aka yi ba to wallahi wannan hare-hare ba zasu tafi ba, kuma suna iya tada Najeriya baki daya, saboda mutanen ba sa tsoron kowa daga jami’an tsaro har hukuma.
“Suna samun kudi, suna bugun kirgi, me zai hana a karkashe su kawai, kowa ya san inda suke.
“Jami’an SSS na bada rahotanni kullum a inda suke, ga abin da suke shiryawa. Abin da nazo sanar wa shugaban kasa kenan.

Gwamna El-Rufai ya ce Idan ba za a yi komai ba, to su a matsayinsu na gwamnoni za su dau mataki da kan su.
Amma a cewar gwamnan a matsayin da ake a yanzu shugaban kasa ya ce cikin watanni komai zai zo karshe.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button