Labarai

Yadda wata copper ta ci mutunci addinin musulunci

Labarin wata copper da As sheikh Dr Abdallah Usman Gadon Kaya ya wallafa a shafin na Facebook yana cewa ta zagi addinin Musulunci wanda ita copper kiristan ce ankaita makarantar kudi a cikin arewarmu wata rana sai ta shirya dirama inda ba baiwa kowane dalibi gefen da zai tattauna akai.
Mutum na farko shine likita ta shirya likita yafito tsaf tsaf a jikinsa wanka mai kyau ya fito a gaban mutane ya fito shiga mai kyau yayi turanci yayi turanci aka tafa masa yace yara ku zamo likitoci.
Mutum na biyu kuma shine lauya inda yaron ya fito da shigar lauyoyi ya fito yayi turanci yayi turanci aka tafa masa anka yaba da irin shigarsa da turancinsa.
Sai dalibi na ukku wanda zai fito yayi bayyani akan muhimmancin  karantun Alkur’ani mai girma sai ta sanya masa rigar mai datti ga annakiya marar kyau ga charbi har kasa rigar daban wandon sa daban da takalmin silifas.
Yaron da ya fito zai nuna muhimmanci karantun Alkur’ani yayi fita mummunar fita wanda duk wanda yaga shigarsa bai son ya zamo mai karantun Alkur’ani ,yayinda yaron yazo yana bayynin Alkur’ani sai copper ta sanya anka fara rabawa manya manya baki kayan shaye shaye “drinks” kenan.
Sai can wani daga cikin mutanen yace kai wallahi wannan ba abun dariya bane anci mutuncinmu an zagi addininmu wannan ba abun dariya bane.
Saboda haka yana da kyau mutane mu kula da irin yadda Kirsitan suke hulda da yaranmu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button