Labarai

Wani dan bindiga ya bada wa’adin kwana 14 a biya shi diyyar matarsa ko ya kashe mutum 300 a zamfara

Wani shugaban yan bindiga ya bada Wa’adin kwanaki 14 a biya shi diyyar matar sa da yan uwanta Naira Miliyan 30, ko ya kashe mutane 300 a Zamfara.

Wani shugaban ‘yan ta’adda da aka fi sani da Nasanda ya yi barazanar daukar fansa kan mutuwar matarsa, kawun ta, da kuma ‘yar uwarta ta hanyar kashe mutane 900 a karamar hukumar Talata Mafara (LGA) ta Jihar Zamfara, Arewa maso Yammacin Najeriya.

Nasanda wanda ya yi sansani a cikin dajin Dumburu na Zamfara, ya ce yana ba gwamnati wa’adin kwanaki 14 ta biya shi diyyar Naira miliyan 30, Naira miliyan 10 ga kowane mutum da ya mutu, daga nan kuma ya bukaci (gwamnatin) ta hukunta Yan Sa Kai, sannan ta tabbatar ba sau cigaba da kashe Fulani ko ‘Yan fashi ba.

Shugaban yan ta’addan, a cikin wani faifan murya da Jaridar HumAngle ta samu, ya bayyana yadda ‘yan Sa Kai, (‘yan banga) da gwamnatin jihar ta haramta suka kashe sabuwar amaryarsa, da kawunta, da kuma kanwarta, bisa laifin da suke zargin cewa suna hada baki da ‘yan ta’adda a yankin.

“Da misalin karfe 11 na dare a Mafara, Yan Sa Kai sun kashe matata, kawunta da kuma kanwarta,” in ji shi.

An kashe matarsa ​​da innarsa nan take. Amma an yanki kawu a idon sawunsa, aka bar shi ya mutu har washegari, sannan aka garzaya da shi asibiti.

Ya ci gaba da cewa, “An yi masa karin ruwa da karin jini kafin ya rasu bayan makonni biyu a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto.”

Nasanda ya yi nuni da cewa idan har maganar kudi ce kuma yana son hadama, da sai ya nemi naira miliyan 50 ga kowane mutum da aka kashe, saidai wannan kawai diyyar rashin adalci da aka yi masa ne. Ya kara da cewa idan aka duba yawan makaman da suke da shi a kungiyarsa, wadanda ba su gaza Naira miliyan 100 ba, za a tabbata ba talakawa ba ne.

“Ba wa’adin watanni zan bayar ba, zan bada kwanaki 14 don biyana diyya. Kuma ba za mu kai hari ba har sai sun shirya yin noma; za mu yi zango a cikin al’ummominsu.”

“Idan an bar Fulani su zauna lafiya, mu ma za mu bar kowa cikin kwanciyar hankali. Idan gwamnati ba za ta iya biyan kudin ba, zan yi abin da na saba yi.”

A cikin shekara ta 2021, lokacin da aka kashe ɗan Nasanda, [Nasanda] ya kashe mutane ɗari don ramuwar gayya. A cikin wannan shekarar ne, lokacin da gwamnati ta shiga cikin fadan sa da wani dan bindiga mai suna Nagala, halan ya yi sanadiyyar da Nasanda ya sace daliban makarantar sakandiren ’yan mata ta gwamnati dake Jangebe a Talatan Marafa ta jihar Zamfara. Sai dai ya saki daliban bayan an biya shi makudan kudin fansa.

Rahoto : Aliyu Samba

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button