Labarai

Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

Yan ta’addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna sama da mako daya sun saki bidiyonsu na farko tun bayan harin da yayi sanadiyar halakar mutum akalla takwas.

A sabon bidiyon da suka saki ranar Laraba, sun bayyana cewa ba kudi suke bukata ba, gwamnati ta san abinda suke bukata.

Sun haska bidiyon ne tare da Shugaban bankin noma, Alwan Hassan, inda suka ce zasu sake shi albarkacin tsufarsa da watar Ramadan.

Ga bidiyon nan kasa.

 

Diraktan bankin BOA da aka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu yanci

Sama da mako guda bayan awon gaba da shi da yan bindiga sukayi a jirgin kasan Abuja-Kaduna, diraktan bankin noma, Alwan Ali-Hassan, a ranar Laraba, ya samu yanci. Bayan harin jirgin da akalla mutane takwas suka rasa rayukansu, iyalan Ali-Hassan suka ce basu ga mahaifinsu ba.

A bidiyon da yan bindigan suka saki, sun bayyana cewa sun saki Alwan Hassan ne bisa yawan shekarunsa kuma albarkacin watar Ramadana.

Source: Legit.ng

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button