Tun bayan mahaifiyar mijina ta fado daki ta tarar muna kwanciyar aure da danta ta daina min magana, Matar aure
Wata mata ta koka akan yadda mahaifiyar mijinta ta dena mata magana bayan ta shiga dakin baccinsu ba tare da kwankwasawa ba, ta tarar da ita da mijinta suna tarayya ta auratayya, labarunhausa na ruwaito
Kamar yadda ta bayyana, lamarin ya auku ne bayan surikarta ta kawo musu ziyara na ‘dan wani lokaci,a cewar Pulse.
Tuko.co.ke ta ruwaito yadda matar ta labarta yadda a duk lokacin da mahaifiyar mijinta na nan take kokarin ganin ta janyo rudani tsakaninta da mijinta.
“A duk lokacin da take nan, tana sa ido akan yadda mijina ke kula dani. Sannan tana tuhumar mijina akan wanne dalili zai bani iko da yawa, musamman wajen yanke shawarar yadda abubuwa ke kasancewa a cikin gidan,” a cewarta, kamar yadda shafin labaran suka yanko maganarta.
Yayin bada labari, ta bayyana yadda dattijuwar matar, lokacin da ta kawo musu wata ziyara, ta banka cikin dakin baccinsu, inda ta tarar da ita da mijin suna biyawa juna bukatar aure.
Kafin aukuwar lamarin mai kama da wasan kwaikwayo a wannnan daren, sirikar tata ta goya jinjirinsu a falonsu, inda jinjirin ya yi bacci a wajen kakarsa.
Saboda haka ne matar da mijinta, wadanda ke uwar daka suka yanke shawarar amfani da damar wajen kusantar juna.
“Sai dai ba tare da tsammani ba, naji jinjirina yana tsala kuka. Naso zuwa in dubashi, amma mijina ya rikeni, gami da cewa sai mun gama abunda muka fara kuma ai mahaifiyarsa na tare da jinjirin,” a cewarta.
Yayin da suke tsaka da jin dadin aurensu, tsohuwar matar ta banko musu cikin daki a fusace ta fara zagin matar ‘danta.
Ta ci gaba da cewa:
“Daga nan, ta fara antayo min ruwan zagi, tare da tambayar wacce irin uwa ce ni, gami da kirana da karuwa, da dai sauran sunayen banza. Duk iya kokarin da mijina ya yi don natsar da ita bai yi tasiri ba, har sai da ya yi mata ihu, saboda sai da ta kai min mari.
“Daga ranar har zuwa yanzu bata kara min magana ba. Mahaifiyata ta umarceni da in bata hakuri. Ban san mai zai faru ba idan na bata hakuri saboda ban mata laifi ba.”
Daga baya uwar mijin ta kai karar sirikarta wajen danginta, inda ta ce ta ci mutuncinta.