Uncategorized

Sojojin Nijeriya sun kashe yan ta’adda 13 tare da raunata wasu da dama a jihar Borno

Sojojin Najeriya na 202 Battalion da ke gudanar da aiki karkashin 21 Special Armoured Brigade sector 1 wadanda ke operation Haɗin kai sun kashe yan ta’adda 13 dake ƙarƙashin kungiyar ta’addanci ta Jama’atu Ahlussunnah lidaawati waljihad a wani hari da sojojin suka kai sansanin yan ta’addan a arewa maso gabashin Borno.

Rundunar ta 21 Special Armoured Brigade dake Bama na karkashin kulawa da sa idon Birgediya Janar Waidi Shayibu, wanda shine General officer commanding (GOC) 7 division na Rundunar sojin kasan Najeriya.

Bataliyar dake ƙarƙashin jagorancin Lt col. Isaac indiorhwer, da hadin gwiwa da CJTF sun farmaki maɓoyar yan ta’addan dake Mallum Masari, Gabchari, Mantari, Kanari, Markas, Garin da Baban baba, duka kauyika ne dake karamar hukumar Bama a ranar 7 ga watan Afrilu, sun kuma kashe yan ta’addan da dama a fito na fito da sukai da su.

Wasu da dama daga yan ta’addan sun gudu tare da raunukan harbin bindiga a jikin su.Sojojin Nijeriya sun kashe yan ta'adda 13 tare da raunata wasu da dama a jihar Borno

Dakarun sunyi nasarar ceto mata 43, yara da kuma wani dattijo da yan ta’addan suka rike a maɓoyar tasu. Sannan sunyi nasarar kwato bindiga ƙirar AK47 guda 9, Magazine ƙirar AK47 guda 6 cike da harsashi mai rai, kekuna da babura da yawa da kuma shanu.

Daya daga yana ta’addan da aka kama a raye wanda ake kira da Abu Asma’u yace su mujahidai ne daga tsagin da Abubakar Shekau ke jagoranta wanda suka tsere daga dajin Sambisa saboda shigowar Sojoji dajin.

Sojojin Nijeriya sun kashe yan ta'adda 13 tare da raunata wasu da dama a jihar Borno

”Muna guduwa daga Sojojin Najeriya ne saboda sun riga sun mamaye mafi yawancin sansanin mu a dajin Sambisa, muna buya a kauyuka ne saboda idan muka gudu zuwa tafkin Chadi, yan ISWAP zasu yake mu” inji sji

A kwanukan nan an samu rahotanni na nasarorin dakarun Najeriya akan yan ta’adda a sansanin su daban daban a arewa maso Gabas na Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka ki ajiye makami daga yan ta’addan na kaura ne zuwa arewa maso yammacin Najeriya kamar Jihohin Zamfara, Sokoto, kebbi, Neja, da kuma Kaduna dan su hada karfi da yan bindiga da kuma yan ta’addan Ansaru.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button