Labarai

Shin Da Gaske Sheikh Dahiru Bauchi yace Gobe sallah?

A yanzu nan ake yada labarin cewa sheikh Dahiru Bauchi yace gobe Lahadi sallah kamar yadda labarin yake yawo a shafukan sada zumunta kamar haka.

YANZU-YANZU: Gobe Lahadi Take Sallah, Cewar Sheik Dahiru Bauchi

Bayan tantancewa da bincike mai zurfi Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya tabbatar da an ga jaririn watan Shawwal a jihohi kamar jaka Birnin Tarayya Abuja, jihar Nasarawa da kuma Kurgwi dake jihar Filato.

Karshe dai Maulana Sheikh ya bada umarni a sha ruwa gobe Lahadi babu Azumi Insha Allahu, domin Azumin bana ya zo karshe..

Maganan Sallan Idi kuwa Shehu ya ce tunda nafila ce a dakata sai ranar da za a yi na gari gaba daya sai a yi tare.

Daga Abubakar Ibrahim”

Amma a bisa haka Hausaloaded sunyi bincike sun gano cewa wannan karya ne duba da shafin shehin malamin ya nuna cewa yana Saudiyya wajen umrah kuma ya wallafa cewa za’a yi sallah a ranar Litinin.

Shin Da Gaske Sheikh Dahiru Bauchi yace Gobe sallah?

Bugu da kari bayyanin wasu muryoyi da ke fita wanda ya nuna cewa na shekarar ya gabata ne shiyasa shafin murya Tijjaniya sunka sanya shehi yayi magana daga Saudiyya Arabia ga abinda yake fadi.

 

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button