Labarai

Shin da Gaske Abubakar malami SAN yayi Murabus daga muƙaminsa?

A yanzu nan muke samun labari daga wasu kafafen sada zumunta inda sunka nuna cewa yayi murabus domin takarar gwamna jihar kebbi.

Dag nan majiyarmu Hausaloaded ta samu wasu labarai masu kamshin gaskiya da ke nuna cewa wannan labari ba gaskiya bane labarin ƙamzon kurege ne kamar yadda Zaidu Bala kofar sabuwa na ruwaito a shafinsa na sada zumunta.

AGF. Abubakar Cika Malami SAN, Shine Ministan Shari’ar Nigeria har yanzu, amma sai gashi wasu Jaridun Najeriya sun buga Labarin Kanzon Kurege wai Abubakar Cika Malami SAN yayi Murabus. Don Allah Jama’a mu daina yada Jita Jita da Labarun Karya.

Suma arewa intelligence sun gudanar da bincike inda sunka nuna wannan maganar ba gaskia bane kamar yadda sunka wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Yanzu nake ganin labari yana yawo sosai a media cewa Maigirma Ministan Shari’a Abubakar Malami SAN ya ajiye mukaminsa na Minista saboda zai tsaya takaran Gwamna a jihar Kebbi

Na gudanar da bincike har zuwa ma’aikatar Shari’a daga tushe, wannan labarin bai tabbata gaskiya ba, yanzu haka ma Maigirma Minista yana cikin ofis dinsa, bai ajiye aiki ba

Muna fatan Allah Ya bamu shugabanni na kwarai ba don halin mu ba.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button