Addini

[sautin Murya] Ba’a san Mace ta zauna a masallaci ta rike lasifika tana karantarwa a zamanin Annabi da Sahabbai ba – cewar Prof. Sani Umar Rijiyar Lemo (Rijiyar Ilimi)

Yadda namiji zai iya isar da ilimi ga duniya a amfana, hakanan ita ma mace yayin da ta tsaya ta natsu ta bada hankalin ta, to ta na gidan ta babu in da ilimin ta ba zai je ba.

Me ya sa za mu ga cewa da yawa hadisan Annabi ruwayar maza ce ba mata ba, babban dalili shi ne mata ko da sun karantu, to yawanci su na ilmantar da ƴaƴan su ne su tarbiyantar da su.

Mace ba ta fiye ta zo MASALLACI ta zauna ta sa kujera ta na karantarwa ba, wannan ba abu ne da aka san shi a lokacin Annabi da Sahabbai ba, a’a yawanci maza ke wannan, mace ko da ta na da ilimi in ba mata sun nema ta a gidan ta ba, to ba ta fitowa ta zo ta shiga Masallaci ta buɗe LASIFIKA ta na karatu ba.

Saboda abinda duk ya shafi aikin waje idan akwai namijin da zai yi shi to ba lallai sai mace ta fito ba.

Saboda asali ta tsare gida da ƴaƴa da yara, da tarbiyantar da su, shi kuma namiji ya tsare waje, idan duk aka yo waje, ita ta yi waje shi ma ya yi waje, to shikenan gidan sai a bar shi babu kowa.

Wannan shi ne abinda Malam ya faɗa da kuma sauran maganganu na ilimi, ban ƙara wa Malam komai ba, sannan ban rage daga abinda ya faɗa ba.

Allah ya sakawa Malam da alheri, ya sa a saurari wannan saƙo da tsarkin zuciya. Ameen.

Ga sautin murya nan kasa.

Dan uwan ku
Abdurrahman Abubakar Sada
13/Ramadhan/1443.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button