Sana’a Goma : Chairman na local Government mai ci yanzu yana sana’ar dinki (hotuna)
Shugaban Karamar Hukumar Birniwa da ke jihar Jigawa kenan me ci a yanzu , da yadukufa wajen Sana ar da yasaba tun Kafin Zaman Shugaba.
Mai girma shugaban karamar hukumar birniwa hon.umar baffa wanda yanzu haka kamar yadda rahoto ya bayyana shine ciyaman mai ci yanzu wanda bai wulakantar da sana’arsa ba.
Wato wannan mutum yana nunawa duniya cewa a duk wani matsayi da ka samu kanka idan akwai lokaci kada ka rena sana’arsa ta asali musamman a fagen siyasa domin kuwa akwai ci akwai faduwa.
Hotunan hon.umar baffa kamar yadda wani marubuci a shafin yanar gizo George udom ya wallafa ya nuna cewa bai je farar da sana’arsa ba.




Wanda Hausaloaded kuma ta samu tabbacin daga wasu mutanen garin da cewa tabbas shine shugaban karamar hukumar birniwa yanzu haka.
Allah Ubangijin yasa mudace mu cire girmankai mu rike sana’a mu da mutunci yafi bara.