Addini

Ramadaniyyat 1443[6] :Azumi Cikin Tsananin Zafi (1) – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

1. Azumin watan Ramadan na wannan shekara ta 1443\2022 ya zo a cikin yanayin tsananin zafi. Sau tari zafin rana yakan wuce daraja 40 a ma’aunin selshiyos (Celsius).

2. Babu shakka yin azumi a irin wannan yanayi mai zafi, yana xauke da dumbin lada ga duk wanda ya tsarkake niyyarsa. Allah (SAW) ya yi wa sahabbai da suka fita yakin Tabuka a cikin tsananin zafi albishir da cewa:
(…Wannan kuwa saboda ba wata kishirwa ko wahala ko yunwa da za ta same su a kan hanyar Allah, kuma ba za su taka wani wuri ba da zai bata wa kafirai rai, kuma ba za su tafka wa abokan gaba wata hasara ba sai an rubuta musu lada saboda shi (wato kowane daya daga abubuwan da aka zana). Lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa). [Tauba, aya ta 120].

3. Don haka duk wata wahala da za ta samu mutum a dalilin biyayya ga Allah, to za a rubuta masa lada a kai, a kuma daga darajarsa.
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yanzu ba na nuna muku abin da Allah yake goge muku kurakurai da shi ba, yake kuma daga daraja da shi?” Sai suka ce: “E, muna so ya Manzon Allah. Sai ya ce: “Cika alwala a lokacin da rai ba ya so (wato lokacin sanyi), da yawan tattaki zuwa masallaci; da jiran salla bayan salla. Wannan shi ne ribadi, wannan shi ne ribadi. [Muslim#252].
Hakanan Annabi (SAW) ya fada wa matarsa A’isha, Allah ya yarda da ita, cewa: “Gwargwadon wahalarki gwargwardon ladanki”. [Muslim#1211].

4. Daga cikin abubuwan da za su dauke wa mumini jin wahalar azumi a cikin wannan yanayi na zafi abubuwa ne guda hudu:

(Za mu ci gaba.)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button