Addini

Ramadaniyyat: 1443 [9]Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya -Dr muhammad Sani Umar R/lemo

Ҝarya wata mummunar halayya ce. Duk wanda aka san shi da ƙarya yakan rasa samun yardar mutane har abada. Don haka, a kowace shari’a aka haramta yin ƙarya. Kuma duk ilahirin masu hankali sun haɗu a kan ganin muninta.
Akwai abubuwa da dama da suke hana mutum ya riƙa yin ƙarya da gangan, ga wasu kaɗan daga ciki:

Na ɗaya, Imani da Allah da ayoyinsa da tsoron haɗuwa da shi ranar alƙiyama, Allah (SWT) yana cewa: (Waxanda ba sa yin imani da ayoyin Allah su ne kawai suke ƙirƙirar ƙarya..). [Suratut Nahl, 105]. Saboda haka riƙo da addini babbar garkuwa ce daga yin ƙarya.

Na biyu, guje wa zubewar mutunci, kamar abin da ya faru lokacin da Hiraƙal shugaban Rumawa ya sa aka kirawo masa Abu Sufyan sarkin Makka da muƙarrabansa, a lokacin bai musulunta ba, ya yi masa tambayoyi game da Annabi (SAW) ya kuma sanar da mabiyan Abu Sufyan cewa, da zarar ya yi ƙarya, su fallasa shi. Don haka, duk abin da Hiraƙal ya tambaye shi game da Annabi SAW sai da ya faɗa masa gaskiya, bai voye masa komai ba, ko ya canza masa, har ma yana cewa: “Na rantse da Allah, ba don gudun kunyar su kama ni na tava yin ƙarya ba, da na yi masa ƙarya”. [Bukhari#7].

Na uku, gudun cutuwa ta fuskar duniya. Wannan shi ne babban dalili da za ka iya samu tare da masu manyan sana’o’i, watau sukan guji yi wa abokan hulɗarsu ƙarya don gudun kada su fahimci suna yi musu ƙarya su canja abokan harƙalla. Don haka, sukan tsaya a kan faɗar gaskiya don guje wa wannan illa. Hakanan ma masu ƙananan kasuwanci, sau tari su ma suna yin gaskiya don sana’arsu ta ɗore kada ƙarya ta ta jawo musu koma-baya a sana’arsu.

Na huɗu, mutumin da ya tashi tun yarinta da neman ilimi, yake kuma fatan kai wa wani matsayi da mutane zu su yarda da shi, su amince da duk wata magana za ta fito daga bakinsa. To irin wannan yakan yi kaffa-kaffa wajen jefa kansa cikin yaɗa labaran ƙarya, don gudun kada iliminsa ya tafi a banza, mutane su daina yarda da shi. Babban Malamin hadisin nan Abdurrazzaƙ As-Sana’ani yana cewa, “Na je aikin hajji, na yi kwana uku babu wani ɗalibin hadisi da ya zo neman hadisi wajena, sai na tafi Ka’aba na yi ɗawafi, na kama rigar Ka’aba ina cewa, Ya Ubangiji, mene ya same ni, shin ni maƙaryaci ne, ko kuma ni mai Tadlisi ne? Sai na dawo gida, sai kuma ga shi sun zo mani”. [Ibn Asakir, juzu’i na 36, shafi na 179].

Don haka malaman hadisi suke guje wa ƙarya don kada su bata ilimin da suka yi shekara da shekaru suna tarawa.
Allah ya sa mu dace. Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button