Addini

Ramadaniyyat 1443 [5] : Babu Ramuwa Ga Wanda Bai Sani Ba – Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

1. Duk wanda ya bar wajibin da bai san da wajabcinsa ba, to ba zai rama abin da ya riga ya wuce ba, a maganar malamai mafi inganci. Daga nan kuma da zarar ya san wajibi ne a kansa, to sai ya aikata shi.

2. Hakanan wanda ya aikata abin da aka hana aikatawa a cikin salla ba tare da ya san hukuncinsa ba, to shi ma ba sai ya rama sallar da da ta wuce ba. Kamar mutumin da ya yi salla a cikin garken rakuma, ko ya ci naman rakumi amma bai sake alwala ba, to wannan ba sai ya rama abin da ya gabata ba.

3. Amma idan mutum ya san da hukuncin wajibi sai ya manta, to sai ya rama idan ya tuna. Annabi (SAW) ya ce: “Wanda barci ya dauke shi bai yi salla ba, ko ya manta, to ya sallace ta a duk sanda ya tuna ta” [Muslim#1103].

4. Amma wanda bai san da wajibi ba, to idan ya sani, sai ya sallaci sallar da lokacin bai fita ba, da kuma mai zuwa. Ba sai ya rama na baya ba.

5. Kamar sa’adda wani bakauye ya yi salla ba daidai ba, sai Annabi (SAW) ya ce masa: “Je ka yi salla, domin ba ka yi salla ba”. Sai ya ce: “Na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya, ban iya wanda ta fi wannan kyau ba, sai ka koyar da ni abin da zai isar mini a sallata”. Sai Annabi (SAW) ya koyar da shi salla. [Bukhari#757 da Muslim#397].

6. Annabi (SAW) ya umarce shi da ya rama sallar da ake cikin lokacinta, amma bai umarce shi ya rama ta baya ba, tare da ya fada masa cewa, bai iya sallar da ta fi wadda ya yi kyau ba.

7. Hakanan bai umarci Umar (RA) da Ammar (RA) su rama sallolinsu ba. Umar (RA) yayin da janaba ta same shi, sai ya ki yin salla gaba daya. Ammar kuwa sai ya yi birgima a kasa kamar dabba ya yi sallarsa.

8. Hakanan sahabban da suka rika cin abinci a Ramadan bayan asuba, har sai da suka rika gane farar igiya da bakar igiya, su ma Annabi (SAW) bai umarce su da ramuwar azuminsu ba.

Duba, Ibn Taimiyya, Majmu’ul Fatawa, juzu’i na 23, shafi na 37-39].

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button